BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Abin da Bala Kaura ya ce kan rade-radin sauya shekarsa zuwa APC
Duk da rikicin cikin gida da jam'iyyar PDP ke fama da shi amma Shugaban jam'iyyar a jihar ta Bauchi, ya ce kansu a haɗe yake yana mai yi ikirarin cewa ana ƙoƙarin neman a razanar da magoya bayansu ne.
Stones zai bar Man City, Tottenham na son Rudiger
Bayern Munich da Chelsea na harin Bart Verbruggen a wannan bazara, John Stones zai bar Manchester City idan kwangilar shi ta ƙare, yayin da Atletico Madrid son ɗauko Marc Cucurella.
Manyan ƴan siyasa da aka bincika a Najeriya bayan hawan Tinubu
A halin yanzu dai wasu fitattun ƴan siyasa musamman daga ɓangaren adawa a Najeriya suna na fuskantar tuhume-tuhume a kotu da suka shafi halasta kuɗin haram da karkatar da kuɗaɗen gwamnati da sauransu.
‘Sun yi wa yarana maza huɗu yankan rago’
Aminata Yameogow ta ce a rana daya aka yi wa yaranta hudu yankan rago sannan kuma tun daga ranar ba ta kara ganin ‘yarta ba.
Abin da majalisar dokokin Amurka ta ce a kan Kwankwaso da Miyetti Allah
Wasu ƴan majalisa na jam'iyyar Republican ne suka gabatar da ƙudurin, wanda a ciki suke kira ga sakataren harkokin wajen Amurka kan ya ayyana wasu ƙungiyoyi ƴan bindiga a matsayin ƴan ta'adda, sannan kuma a sanya takunkumi kan wasu ƴan Najeriya.
Najeriya za ta tura dakaru na musamman zuwa jihohin Kwara da Neja
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 11 ga watan Fabrairun 2026.
Mutumin da ke ƙirƙiro wa Trump manufofin da ke jawo cece-kuce
Turjiyarsa da kuma ba ji ba gani a ɓangaren tsare-tsaren fadar White House, su suka janyo Trump ya ki sassautawa ƴan ci-rani kuma ya samu wani ƙarfi na gaske wajen faɗaɗa ikon Amurka a faɗin yankuna.
Abin da muka sani kan tura ƙarin sojojin Amurka 200 zuwa Najeriya
"Waɗannan sojoji ba za su shiga fagen daga ba kuma ba za su fafata ba kai-tsaye," a cewar mai magana da yawun shalkwatar tsaron Najeriya.
Ƙasashe 10 da suka fi fama da cin hanci da rashawa a duniya
Ana tantance matsayin rashawa a kowace ƙasa ne ta hanyar la'akari da makin ta suka samu, daga 0 zuwa 100. Maki 0 na nufin ƙasa na cikin matsanancin rashawa, yayin da maki 100 ke nufin ba ta da matsalar rashawa.
Abin da ya kamata ku sani kan azumin Ramadan na 2026
A ranar 18 ko 19 ga watan Fabrairun 2026 ne ake sa ran al'ummar Musulmi a faɗin duniya za su tashi da azumin watan Ramadan na wannan shekara.
Abin da ya sa na ajiye shugabancin NAHCON - Abdullahi Saleh Pakistan
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 10 ga watan Fabrairun 2026.
Me ya sa ake wahalar ruwan sha a cikin birnin Kano?
Al'ummar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, musamman cikin birnin jihar ana fuskantar matsalar karancin ruwa sha, lamarin da ke tilastawa magidanta sayen ruwa daga masu tura kurar ruwa.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Hantsi, 06:30, 12 Fabrairu 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 12 Fabrairu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 11 Fabrairu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 11 Fabrairu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Wasanni
KAI TSAYE, Ronaldo bai buga wa Al Nassr wasa ba, amma ya yi atisaye a Riyadh
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Lahadi 08 zuwa 13 ga Fabrairu 2026
Yaushe wannan masoyin Manchester United ɗin zai yi aski?
''Na zaci cewa abin ba zai wuce wata uku zuwa huɗu ba, ashe na yi kuskure a hasashena," kamar yadda Ilett ya shaida wa BBC.
Maguire ba zai bar Man Utd ba, Al-Ittihad na son Salah
Aston Villa za ta yi zawarcin Morgan Gibbs-White, Ƙungiyoyin Saudiyya na farautar ɗanwasan gaba na Liverpool Mohamed Salah, yayin albashin Sandro Tonali ke neman zama cikas ga ƙungiyoyin Serie A da ke son ɗanwasan.
Ronaldo ya gama yajin taka leda, Ko Zidane zai dawo Madrid?
Cristiano Ronaldo zai dawo murza leda a Saudiyya, Sauyin shugabanci a Barcelona zai tabbatar da makomar Marcus Rashford a Spain, Zinedene Zidane zai iya komawa Real Madrid.
Yadda ƴanmata ke shiga ƙwallon ƙafa don guje wa auren dole
Wasu ƴanmata ƴan uwan juna biyu a Indiya sun bayyana yadda kwallon kafa ya sauya rayuwarsu da kuma taimaka musu wajen yaki da auren wuri.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kashe ƙwarƙwatar ido
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Kududdufin da ba ya cika kuma ba ya ƙafewa a Najeriya
Akwai rafuka da tafkuna da dama a duniya, kuma Najeriya ma na da irin nata, waɗanda wasun su ke da abubuwa na ban al'ajabi.
Wace dabara ta rage wa Iran idan tattaunawa da Amurka ta gaza aiki?
Tattaunawar na zuwa ne a daidai lokacin da barazanar yaƙi tsakanin Amurka da Iran ke ƙaruwa.
Yadda APC ta fara faɗawa tarkon rikici a jihar Kano
Kurar rikici ta fara turnuƙewa a jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kano, da ke arewacin Najeriya, makonni bayan sauyin sheƙar gwamna Abba Kabir Yusuf. An fara ganin ƙurar ne a tarukan haɗa kan 'ya'yan jam'iyyar APC tsoffi da sabbi a cikin wasu ƙananan hukumomin jihar.
Wace dokar zaɓe ake taƙaddama a kai kuma me ya sa aka ƙi amincewa da ita?
Ƙungiyoyin fararen hula da ƴan adawa da kuma na mata na can sun bazama kan tituna a Abuja, babban birnin Najeriya domin adawa da kin amincewa da sashen da ya ba da damar aika sakamakon zaɓe ta na'ura da majalisar dattijan Najeriya ta yi.
An kai ƙarar Instagram da YouTube kan 'mallake tunanin yara'
Kamfanonin sada zumunta biyu mafi girma a duniya na fuskantar tuhuma kan samar da shafukan da suka zamo "alaƙaƙai" ga yara yayin da aka fara sauraron ƙarar da aka shigar a Amurka.
Me ya sa shigar malamai siyasa ke janyo muhawara a arewacin Najeriya?
Wannan ba shi ne karon farko da shigar malaman addinin Musulunci harkar siyasa ya janyo muhawara a tsakanin al'umma ba.
'Nakan ji kunyar shiga mutane saboda manyan nonuwana'
Yayin da masu manyan nonuwa ke jan hankalin mutane a sassan duniya da dama, ta wani ɓangare kuma ya kan shafi lafiyar mata da kuma ingancin rayuwarsu.
Za mu kawar da barazanar ƴanbindiga a Najeriya - Tinubu
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 9 ga watan Fabrairun 2026.
Yadda mayaƙa ke inganta salon kai hari da jirage marasa matuƙa a Najeriya da wasu ƙasashen
Ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi na ƙara yawan ahare-haren da suke kaiwa ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa a Najeriya da ƙasashen Yammacin Afirka.
Bukatunmu kan gyaran dokar zaɓen Najeriya - El-Rufai
Tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai kuma jigo a jam'iyyar hamayya ta ADC, ya ce suna son a amince da dokar zaɓen da Majalisar Wakilai ta amince.
Cututtukan da za a iya ɗauka a wajen kitso ko aski
Mako-mako ko wata-wata ko kasa da haka, kowa na da lokacin da yake dauka kafin ya je a rangada masa aski ko kuma a rangada mata kitso, sai dai wani lokaci idan ba a dauki matakan da suka kamata ba, a garin neman gira sai a rasa ido.
Yadda ni da mijina muka yanke shawarar yin soyayya da wasu mutane na daban
Dakta Ilana Elea wadda ta kasance marubuciya kuma mai koyarwa, ta bijiro da wani batu tsakaninta da mijinta wanda zai sauya rayuwar aurensu: Yin soyayya da wasu mutane na daban.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.



































































